Ƴan sanda sun mamaye hanyoyin babban birnin Abuja sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce tana aiki tuƙuru don tabbatar da kare rayukan jama’ar babban birnin ƙasar Abuja, inda hare-haren ƴan bindiga ke ƙara zafafa a baya-bayan nan.
Rundunar ta ce tuni babban sipeton ‘yan sandan ƙasar ya ba da umarnin ƙara baza jami’an tsaro a sassan birnin don tabbatar da wannan aniya.
Ta kuma buƙaci jama’a a birnin su taimaka mata da bayanan sirri domin samun nasarar abun da aka sanya a gaba.
Wasu ma’aikatan BBC da suka tashi daga aiki da daren ranar Talatar nan, sun tabbatar da ganin an rufe wasu manyan hanyoyi, inda mutane ke kewayewa suna bi ta wasu hanyoyi.
A baya bayan nan dai ana ta samun karuwar hare-haren yan bindiga a Najeriya, musamman a garuruwan da ke kewaye da birnin, inda maharan ke kashe jama’a, suna garkuwa da wasu da dama.