Gargajiya a ƙasar Hausa

0
423

KACIYA

A gargajiyace, akan yi kaciya a ƙasar Hausa wadda wanzamai suke wanzarwa. Ana tattara yara masu shekaru ɗaya, a yi wa dukkansu kaciya a rana guda. Wani ƙwararre, mai suna Wanzami ya na amfani da kayan aikinsa don aiwatar da aikin, yayin da sauran yara ke samun kariya daga gani, (don kar su razana). A kan yi amfani da, aska, da ruwa, da sabulu, da sauransu wajen yin Shayi ko Kaciya.

Kaciya

ƘAHO

Ƙaho, tiyata ce ta gargajiya da masu sana’ar aski, watau wanzamai na Hausawa ke yi, ta hanyar amfani da ƙaho, wadda aka fi sani da, “tsarin cire cuta daga jiki.” Wani jini ne da ke fitowa baƙi daga jiki, jinin ya kasance mara kyau ne.Ƙaho, ita ce hanyar gargajiya da ake bi wajen tattaro da cire cututtukan gaɓɓan jiki.

Ƙaho

GANUWA

Ganuwa, gini ne da ake zagaye gari da shi domin samun kariya daga harin abokan gaba da kuma sauran dabbobi masu cutarwa a zamanin da can-can baya.

Ganuwa

SHURI

Shuri, tarin ƙasa ce da ƙwari irin su tururuwa da sauran dangoginsu suke samarwa idan suka daɗe a wuri.A ƙasar Hausa, an camfa shuri da cewa matattarar iskokai ne, saboda haka a zamanin da can baya, ba kowane mutum ne yake iya zuwa ko gindinsa ba ma ballantana ya cire shi.

shiri

Leave a Reply