Gabanin wasan Najeriya da Afirka ta Kudu, an buƙaci ‘yan Najeriya mazauna ƙasar da su yi taka-tsan-tsan

0
123

Daga Maryam Umar Abdullahi

Ƙasashen biyu dama sun daɗe da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana’antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, kuma kusan su ne mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar.

Hukumomin Najeriya a jiya Talata sun yi ƙira da a yi taka-tsan-tsan kan abin da suka bayyana a matsayin “barazana” ga ‘yan ƙasar su da ke zaune a Afirka ta Kudu gabanin haɗuwar ƙasashen biyu a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka – wasan ƙwallon ƙafa da ke sabunta takun saƙa.

Sai dai a yanzu zaman ɗar-ɗar na ƙaruwa a fagen wasan ƙwallon ƙafa yayin da Najeriya da Afirka ta Kudu ke shirin buga wasan kusa da na ƙarshe a Ivory Coast ranar Laraba.

Babban Ofishin Diflomasiyyar Najeriya a Afirka ta Kudu ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan Afirka ta Kudu na yin kalamai masu tayar da hankali a yanar gizo waɗanda akasarinsu “sun ƙunshi barazana” ga ‘yan Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba – ECOWAS

Ofishin harkokin diflomasiyya ɗin ya buƙaci ‘yan Najeriya mazauna ƙasar Afrika ta Kudu da su kula da kalamansu, su lura da inda za su je kallon wasan… kuma su guji shiga cikin hayaniya, tarzoma ko tada hankali idan Super Eagles (laƙabin tawagar ‘yan wasan kwalon Najeriya) suka lashe wasan kusa da na karshen.”

Sashen hulɗa da ƙasa da ƙasa na Afirka ta Kudu ya ce ƙasar “ba ta amince da fargabar da aka bayyana ba” a cikin sanarwar, in da ta ƙara da cewa: “Shawarar abin takaici ne saboda da alama ta haifar da zaman ɗar-ɗar tsakanin ‘yan ƙasar Afirka ta Kudu da ‘yan Najeriya mazauna ƙasar ko kuma bakin da su ka zo ziyarar Afirka ta Kudu.”

A cikin 2019, tashin hankali mai nasaba da ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu ya yi sanadin mutuwar mutane 12.

Najeriya da Afirka ta Kudu za su sake haɗuwa ne a wasan kusa da na ƙarshe kamar yadda suka haɗu a shekarar 2000, inda Najeriya ta yi nasara da ci 2-0. Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a karo na uku a shekarar 2013, yayin da Afirka ta Kudu ta samu nasara a shekarar 1996.

Leave a Reply