Lionel Messi ya ce farin cikinsa ya dawo tun bayan komawarsa ƙungiyar Inter Miami.
Messi ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, inda ya ce komawarsa Amurka ta sha bambam, idan aka kwatanta lokacin da ya koma Paris Saint-Germain (PSG) ta Faransa daga Barcelona.
Ya zura ƙwallaye tara a cikin wasanni shida tun ya koma Inter Miami, bayan shafe shekara biyu da PSG a Faransa.
“Kamar yadda na faɗa a lokacin, komawa ta Faransa ba abu ne da na so ba, saboda ba na son barin Barcelona,” in ji Messi.
Ya ce yana jin daɗin rayuwa kudancin Florida a yanzu.
KU KUMA KARANTA: An dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nwokocha daga wasanni kan amfani da haramtattun ƙwayoyi
“Na sha wahala wajen sabawa da wurin da ya sha bamban da inda na shafe tsawon rayuwata ina zaune, musamman ma yanayin birnin da kuma ɓangaren wasa, gaskiya abu ne da na wahala, amma a yanzu saɓanin haka nake gani a Amurka,” in ji shi.
Messi mai kyautar Ballon d’Or bakwai yana da damar lashe kofinsa na farko da Miami yayin da za ta fafata da Nashville a wasan ƙarshe na Leagues Cup a ranar Asabar.