El-Rufai ya kori sarakuna biyu da hakimai uku, a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki

0
332

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya amince da tsige sarakunan Piriga da Arak, Jonathan Paragua Zamuna da Janar Aliyu Iliyah Yammah (mai ritaya).

Kwamishinar ƙananan hukumomin jihar, Hajiya Umma Ahmad ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce daga ranar Litinin, 22 ga Mayu, 2023 sarakunan biyu sun daina gudanar da ayyukan su na ofisoshinsu.

A cewar sanarwar hakan ya biyo bayan shawarwarin da ma’aikatar ƙananan hukumomi ta bayar ne bisa tanadin sashe na 11 na dokar cibiyoyi ta gargajiya mai lamba 21 na shekarar 2021.

Ya ce, “Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, shi ne zai kula da al’amuran masarautar Piriga, har zuwa lokacin da za a naɗa sabon basarake, yayin da aka umurci Sakataren Majalisar da ya fara aikin naɗin sabon Hakimi.

KU KUMA KARANTA: El-Rufa’i ya rushe asibiti, makarantu da gidajen jama’a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki

“Gomna Ahmadu, sakataren majalisar masarautar Arak kuma, zai kula da al’amuran masarautar sannan kuma zai fara aiwatar da naɗin sabon hakimi.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “gwamnati ta ga irin martanin da Janar Iliyah Yammah ya bayar game da batun naɗin hakimai huɗu, saɓanin wanda aka amince da shi a masarautarsa, da rashin zama a masarautar Arak.

“Yayin tsige Jonathan Zamuna ya biyo bayan rikicin ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin al’ummar Gure da Kitimi na Piriga a ƙaramar hukumar Lere, da rashin zama a cikin masarautar.”

Haka kuma ta sanar da sallamar hakiman ƙauyukan Aban, Abujan Mada da Anjil da ke masarautar Arak.

Leave a Reply