El-Rufai ya kai ƙarar Majalisar Dokokin Kaduna kotu

0
101
El-Rufai ya kai ƙarar Majalisar Dokokin Kaduna kotu

El-Rufai ya kai ƙarar Majalisar Dokokin Kaduna kotu

Daga Idris Umar, Zariya

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El’rufai, ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna da Gwamnatin Jihar a Kotun High Court dake Jihar, kan zargin bata suna da sharri.

Nasiru El’rufai, ya shigar da ƙarar ne a safiyar yau Laraba, inda ya nemi Kotu ta bi masa kadin cin zarafin da take hakki da Kuma sharri.

Hakan ya biyo bayan zargin da Gwamnatin Jihar Kaduna tayi kan cewar tsohuwar Gwamnatin Malam Nasiru El’rufai, ta wawure Nera Biliyan 423 a lokacin tana gudanar da mulkin, a tsakanin rancen kuɗaɗe da bayar da ƙwangila da Kuma zarar kudade tsurar su wato (Cash) a turance.

KU KUMA KARANTA: Majalisar jihar Kaduna za ta ɗauki mataki kan yaron El-Rufa’i

Kafin yanzu majalisar dokokin jihar Kaduna, ta kafa Kwamitin membobin ta guda 13 da suka binciki tsohuwar Gwamnatin tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2023, wanda daga ƙarshe rahotan ƙwamitin ya kama El’rufai da wasu daga cikin makarraban Gwamnatin sa da cin amanar Gwamnati da Kuma handama da babakere.

Duk da dai El’rufai ya musanta har ma ya danganta hakan da siyasa ce tsagoronta.

Leave a Reply