EFCC ta bankaɗo sabuwar badaƙala kan Yahaya Bello

0
40
EFCC ta bankaɗo sabuwar badaƙala kan Yahaya Bello

EFCC ta bankaɗo sabuwar badaƙala kan Yahaya Bello

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gabatar wa wata Babbar Kotu a Abuja sabbin tuhume-tuhume 16 da suka shafi zamba da take zargin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya aikata.

Tuhume-tuhumen da Gwamnatin Tarayya ta shigar ta hannun lauyoyin EFCC, Kemi Pinheiro da Rotimi Oyedepo da wasu lauyoyi 7, sun ƙara haɗa Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu a matsayin waɗanda ake zargi tare da Yahaya Bello.

Lamarin dai na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan ya ke ’yar wasan ɓuya da mahukunta EFCC da kuma ƙin halartar wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da suke tuhumarsa kan sace zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 80.2 a lokacin da yake riƙe da madafun iko a jihar.

KU KUMA KARANTA: Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya amsa gayyatar EFCC

A ƙunshin sabbin tuhume-tuhumen, EFCC ta bayyana cewa ta bankaɗo wani sabon zamba da ake zargin tsohon gwamnan da ya kai har N110,446,470,089.00.

Leave a Reply