EFCC a Abuja ta kama ‘yan China 4 bisa zargin damfarar Intanet

0
30
EFCC a Abuja ta kama ‘yan China 4 bisa zargin damfarar Intanet

EFCC a Abuja ta kama ‘yan China 4 bisa zargin damfarar Intanet

Jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta kama mutane 105, ciki harda ‘yan China 4, a wani ginin kasuwanci dake yankin Gudu na birnin Abuja.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a yau Juma’a.

KU KUMA KARANTA:Hukumar EFCC ta kori jami’anta 27 daga aiki

A kokarin da su ke yi na tsaftace Najeriya daga damfarar intanet da sauran nau’ukan zamba, jami’an hukumar EFCC, sun kama ‘yan China 4 da wasu ‘yan Najeriya 101 a wani ginin kasuwanci da ke yankin Gudu na birnin Abuja,” a cewar hukumar EFCC.

Ya kara da cewa an kama wadanda ake tuhumar ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairun da muke ciki, inda yace sun hada da maza 67, ciki har da ‘yan Chinar, da kuma mata 38.

Leave a Reply