Duk wani juyin mulki idan ya samu awa 24, to ya zaunu – Dakta Hassan Gimba a hirarsa da RFI Hausa

1
376

Daga Ibraheem El-Tafseer

Duk wani juyin mulki, idan ya samu awa 24, to ya zaunu. Wannan kalami ya fito ne daga bakin fitaccen ɗan jaridar nan kuma marubuci, mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba, a hirarsa da RFI Hausa ranar Litinin, kan juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Ya ci gaba da cewa “mutanen da sun yi naɗe-naɗe, sun kawo wani daga Bankin raya Afirka ya zo musu (prime minister), sun naɗa wannan, sun naɗa wancan, ai gwamnati ta riga ta zauna. Tun farkon fari ba a bi abun yadda yakamata a bi ba, kamar yadda Bahaushe yake cewa “an yi sake ɗan Zaki ya girma” yanzu sai dai a lallaɓa su, a samu zaman lafiya”.

Tambaya: An tura ƙungiyar yammacin Afirka domin zaman lafiya, amma suna ta furta waɗansu irin kalamai?

Ai dole su furta kalamai, domin gwamnatinsu ta riga ta zauna, gwamnati ne yanzu mai ci. Kawai dai a san yadda za’a yi a dawo da harkoki kamar na kullum, idan ba haka ba, aka ce za’a ci gaba da takunkumi, sai dai ‘yan ƙasa ɗin su wahala, manyan gwamnati ba zai shafe su ba.

NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar

Tambaya: Majalisar Ɗinkin Duniya ECOWAS suna ƙira sojojin, domin a samu maslaha, ba ka ganin suna da kyakkyawar manufa ga Nijar?

Babu wanda zai ce babu kyakkyawar manufa, amma kuma ‘yan ƙasar ne suka ce ga abin da suke so. A lallaɓa ka da jama’a su wahala, ka da bayin Allah su tagayyara.

KU KALLI BIDIYON ANAN

Cikakken bidiyon hirar Dakta Hassan Gimba da RTF Hausa

Tambaya: A halin da ake ciki na sulhunta wa, shi kuma jagoran Sojojin Nijar, ya ma fara batun tsara gwamnatin riƙon ƙwarya, waɗanda za su shafe shekaru uku kan karagar mulki. Shekaru uku a mulkin Soja?

Shekaru uku a mulkin soja ai kamar kwana uku ne. A nan Afirka ba mu ga gwamnatocin Soja inda suka yi shekaru ba? Ko a su ECOWAS akwai waɗanda sun yi shekaru 20, wasu ma 30. Su me za ka ce musu? Sai dai fa a lallaɓa indai ba yaƙi za’a yi ba.

Tambaya: Ka ambaci kalmar yaƙi, wanda Ecowas ta ce ana kan tsara shi?

To shi yaƙi kamar tafiya ne, kai ne da shi, amma ba ka san ƙarshensa ba, haka yaƙi yake. Idan ka fara shi, ba ka san yadda zai ƙare ba. Yanzu alal misali Najeriya, idan ta ce za ta yi yaƙi. Mu kuma fa muna fama da matsalar rashin tsaro. Idan muka buɗe kafa na yaƙi, waɗanda a kudu da suke neman ɓantarewa, Arewa maso gabas da su ma suke neman ɓantarewa, wai su ma suna jihadi. Arewa maso yamma, ana ta fama da masu garkuwa da mutane, su ma kansu ‘yan Boko Haram ne, suna neman ɓantarewa. To da wanne za mu ji?

Idan muka mayar da hankalinmu wai muna yaƙi, shikenan an bar baya da ƙura. Kamar kana tafiya ne, wuta tana cinye ka ta baya.

Tambaya: Idan ana buƙatar dawo da tsarin Dimokraɗiyya a Nijar, ba tare da an kai ruwa rana ba, yaya za’a yi?

Sai a tafi da su waɗannan mutanen gwamnatin, waɗanda yanzu suke kai.

1 COMMENT

Leave a Reply