DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sanar da jama’a cewa ta kama wasu mutum biyu Sharu Abubakar Tabula da Isma’il Iliyasu Mangu bisa laifin tayar da rikici a wasu sassan jihar Kano da gangan.

Hukumar tabbatar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Peter Afunanya, Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar wanda ya fitar a ranar 15 ga Maris, 2023.

Sanarwar ta ce waɗanda ake zargin sun aike da sakwannin da za su iya cutar da al’umma, waɗanda suka yaɗa ta kafafen sada zumunta daban-daban.

Yace a cikin sakonnin masu cutarwa, sun yi kira na musamman ga wasu muradun siyasa tare da yin kira kai tsaye ga magoya bayansu da su kai farmaki ga masu adawa da su, ciki har da jami’an tsaro yayin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi ranar 18 ga Maris, 2023 a jihar.

KU KUMA KARANTA: Zamu yi maganin duk wanda ya fito da makami komai girmansa- DIG ga ‘yan siyasa

“A sakamakon wannan lamari, wata jam’iyyar siyasa ta Kano ta yi barazanar shirya zanga-zangar a cikin babban birnin tarayya da kuma ofisoshin wasu jami’an tsaro a ranar 16 ga Maris, 2023 domin nuna goyon bayan ga waɗanda aka kaman.

“Yayin da hukumar mu ke faɗakar da jama’a game da wannan shirin ba bisa ƙa’ida ba, muna kira ga wanda abin ya shafa da su janye shirin nan da nan ko kuma su shirya fuskantar sakamakon.” In ji sanarwar.

Hukumar DSS ta ba da tabbacin cewa ba za ta zuba ido tana kallon ɓata-gari ko ƙungiyoyi suna barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar ba.

Ya ce kamata yayi shugabancin jam’iyyar su riƙe ‘ya’yan jam’iyyar tare da jan hankalinsu da su guji gudanar da ayyukan da za su haifar da taɓarɓarewar doka da oda a Kano da kewaye kafin lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓen da aka tsara.

Sanarwar ta ce halin da ake ciki, Hukumar ta na haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an samar da isasshen tsaro domin gudanar da zaɓen cikin nasara.

Baya ga Kano, kwanan nan Hukumar ta kama wasu ’yan ta’adda masu yin barazana ga tashin hankali a wasu Jihohin Tarayya, idan za a iya tunawa cewa a ranar 8 ga Maris, 2023, hukumar umurci ‘yan siyasa da su yi aiki mai ma’ana kuma su guji tashin hankali, da yaɗa labaran karya, da kalaman ƙiyayya, ta kuma sake nanata kira ga ‘yan siyasa da su yi biyayya ga wasiƙun dokar zabe da jagororin zaɓen suka rattabawa hannu.

“Ana shawartar kowa da kowa da su bayar da gudummawar gaske don samar da zaman lafiya da dimokuraɗiyya a Najeriya”. In ji sanarwar hukumar DSS.


Comments

3 responses to “DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta”

  1. […] KU KUMA KARANTA: DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *