Dorinar ruwa a Kebbi ta yi sanadiyar mutuwar wani mutum

0
29
Dorinar ruwa a Kebbi ta yi sanadiyar mutuwar wani mutum

Dorinar ruwa a Kebbi ta yi sanadiyar mutuwar wani mutum

Daga Idris Umar, Zariya

Wata dorinar ruwa mai jego, ta yi sanadin mutuwar wani bawan Allah mai gadin lambun Sarkin Yawuri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi, a yayin da yake kamun kifi a cikin kwale-kwale, a wani rafi inda yaci karo da wata dorinar ruwa wacce bata jima da haihuwa ba, ta fito daga cikin ruwan wanda Malam Usman bai kula da wannan dorinar ba, sai ta auka masa inda ta samu nasarar ji masa rauni mai girman gaske.

Wani rahoto ya nuna cewa, dorinar ta haihu ne ba jimawa bisa haka ta zama cikin hushi na soyayyar dake tsakaninta da ɗan da ta haifa.

Wannan lamarin ya faru ne a ƙauyen Tillo da ke ƙaramar hukumar Yawuri da yammacin jiya lahadi.

KU KUMA KARANTA: Yadda rago ya ɓace a motar haya daga Bauchi zuwa Kano

Gwamna jihar, Nasir Idris na jihar Kebbi ya jajantawa masarautar Yawuri da iyalan Malam Usman mai-gadi, wanda ya rasa ransa.

Gwamnan ya shawarci masarautar da su karɓi ƙaddara haka Allah ya so. Gwamnan yayi addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma ba shi Jannatul Firdaus.

An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Leave a Reply