Donald Trump ya musanta zargi da yuhume-yuhume 34 da ake masa

0
260

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa, a ranar Talata da ta gabata, bayan da aka kai shi hannun ‘yan sanda a ofishin Lauyoyin gundumar Manhattan domin gurfanar da shi a gaban kotu, in ji CNN.

Wannan ya sanya shi ya zama tsohon shugaban Amurka na farko da aka bincika, ko kuma tsohon shugaban Amurka da ya fuskanci tuhume-tuhume a tarihin ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta umarci jihar Ondo da ta biya diyyar naira miliyan 30 ga mutumin da ‘yan Amotekun suka harbe

A wani ɓangare na kamun nasa, ana sa ran za a yi wa shugaba Trump ɗin hoton yatsa, ko da yake ba a san ko za a ɗauki hoton nasa ba. Sai dai Trump a cikin sirri ya nuna sha’awar a ɗauki hotonsa, a cewar majiyoyi biyu na kusa da batun.

Sannan za a gurfanar da shi a gaban wata kotu a birnin New York, wanda rahotanni ke cewa zai kasance cikin gaggawa da tsari.Har ila yau, ba a daure masa hannu da ankwa ba, bayan kama shi kuma zai ci gaba da kasancewa ƙarƙashin kariya ta tilasta bin doka.

Bayan da wata babbar Alkali ta tuhume shi a hukumance a makon da ya gabata. Trump ya mayar da martani kan tuhumar da ake masa na cewa yana da hannu a cikin shirin kashe kuɗi a yakin neman zabensa na shekarar 2016 bayan an same shi da tuhume-tuhume 34 a shari’ar Stormy Daniels.

Donald Trump ya kira tuhumar da “sharrin ‘yan siyasa” kuma ya zargi ‘yan Democrat da “kasancewa munafikai.” Ya ci gaba da cewa ba shi da wani laifi kuma ya yi iƙirarin cewa shi ne wanda aka azabtar da shi a wata farautar mayya ta siyasa wanda mai shari’a Alvin Bragg da kuma shugaban ƙasa na yanzu Joe Biden suka jagoranta.

“Na yi imanin wannan mayya-Hunt za ta mayar da martani ga Joe Biden,” in ji tsohon shugaban. “Mutanen Amurka sun fahimci ainihin abin da ‘yan jam’iyyar Left Democrats ke yi a nan. Kowa na iya gani.

Don haka Ƙungiyarmu, da Jam’iyyarmu, za su haɗa ƙarfi, za su fara kayar da Alvin Bragg, sannan za mu kayar da Joe Biden, kuma za mu kori kowane na ƙarshe daga cikin waɗannan ‘yan jam’iyyar Democrats daga ofis ta yadda za mu iya SAKE DAUKAKA KASAR AMERICA!” inji shi.

Leave a Reply