Dogayen layukan mai sun sake bayyana a birnin Abuja

Dogayen layukan sayen mai sun sake bayyana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, abin da ya jefa masu motoci cikin damuwa.

Tun daga ranar Talata ne matsalar ta sake bayyana wadda daman brnin ya yi fama da ita a cikin shekarar nan, lamarin da ya sa masu ababan hawa ke kokawa a kan matsalar.

Ana iya ganin dogayen layukan motoci a wasu gidagen sayar da mai biyu da ke daura da hedikwatar kamfanin mai na Najeriya a tsakiyar birnin na Abuja.

Sakamakon karancin man masu sayar da shi a gefen titi, a jarkoki sun sake bayyana a manyan titunan cikin birnin, inda suke sayar da galan mai cin lita 10 a kan Naira 2,500 zuwa 3,000.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani mai mota, mai suna Umar da ta yi hira da shi ya ce ya sayi man a kan Naira 300 lita daya a wajen babban birnin.

Hukumomin Najeriya sun ce ambaliyar ruwa da ta auku a hanyar Lokoja ce ta sa jinkirin motocin dakon mai zuwa arewacin Najeriya daga Lagos da sauran wuraren da ake dauko man.

Wata kungiyar masu dakon man kuma ta ce lalacewar hanyar jihar Naija ma ta kara ta’azzara matsalar sufurin man zuwa arewacin Najeriyar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *