Direban keke napep ya kashe fasinja a kan naira hamsin

1
257

Daga Haruna Yusuf

Wani matuƙin Keke Napep da ya samu saɓani da ɗaya daga cikin fasinjojin sa kan kuɗi Naira 50 ya kashe shi har Lahira.

Ana cikin rashin fahimta ne aka ce ya kai hannu ya samo wani abu mai kaifi, wanda ya yi amfani da shi wajen daɓa wa mutumin da har yanzu ba a tantance ba ya mutu ko yana raye.

An ce ɗan keken Napep ɗin ya daɓa wa ɗaya daga cikin fasinjojinsa wuƙa har Lahira bayan taƙaddamar da ta ɓarke a tsakaninsu kan Naira Hamsin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane 40 Bisa Tozarta ‘Yan uwansu Masu Keke-napep

A bisa rashin jin daɗinta da matakin da ɗan keke Napep ɗin ya yi na kashe mutumin da ba a san ko wanene ba, mazauna yankin da abin ya shafa suka tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kashe na farko da duwatsu.

Ba a iya tantance sunayen waɗanda suka mutu ba har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Bayelsa (PPRO), Asinim Butswat ya yi Allah wadai da kisan da mahayin Keke Napep ya yi wa matashin tare da kashe shi.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tura jami’an yaƙi da tarzoma domin dawo da zaman lafiya a Kpansia da kewaye, kan kisan gillar da wani matashin mai babur ya yi wa wani matashi a unguwar.
“Matuƙin babur ɗin ya daɓa wa matashin wuƙa har Lahira saboda wata ‘yar rashin jituwa.

“Rundunar ‘yan sandan ta yi Allah-wadai da matakin da direban babur ɗin ya yi, wanda kuma wasu fusatattun matasa suka kashe shi har Lahira tare da yin ƙira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu,” in ji kakakin ‘yan sandan.

1 COMMENT

Leave a Reply