Daraktan Galaxy, Farfesa Muhammad Bello ya taya Ministan Sadarwa Pantami murnar samun lambar Yabo ta CIISec

2
299

Farfesa Muhammad Bello Abubakar, Manajan Darakta na Cibiyar Galaxy Backbone, ya taya babban Ministan Sadarwa Zamani da tattalin arziki na Najeriya Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami murnar samun lambar yabo ta (CIISec) Charted Institute of Information Security.

Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya aika da saƙon taya Ministan Murnar ne ta wajen mai taimaka masa na musamman a bangaren yaɗa labarai Tasiu Muhammad Pantami, inda yace Ministan ya cancanci fiye da haka.Yace wannan lambar yabo Minista Pantami, yana cikin mutane 89 a duniya da suke da wannan lambar su yan kasar Afirka basu da yawa.

A cewar Tasiu Pantami, MD Galaxy, ya bayyana Ministan ne da haziƙin Minista wanda ya kawowa wa ƙasar sa ci gaba mai ma’a a bangaren sadarwar zamani tun shigar ofis a matsayin Ministan Najeriya wanda ya maida hankali sosai akan abunda ya shafi harkar tsaron kasa ta bangaren kimiyya da hakan kuma ya haifar da ‘Da mai Ido.

Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya yabawa cibiyar CIISec na yadda suka zakulo Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami Ministan sadarwa ganin yadda ya mayar da hankali wajen ci gaban kasa da kula da harkar sadarwar yanar gizo dan ci gaban duniya baki daya suka karrama shi da wannan lambar yabo.

Daga nan sai yace CIISec su kadai ne cibiyar kula da harkar sadarwa ingantacciya da suka samu izinin masarautar kasar Uk tun a shekara ta 2018 da aka daurawa alhakin kula da kwarewar harkar da ta shafi bangaren sadarwa kuma sune suka karrama Ministan.Sannan sai ya sake yin amfani da damar ya sake taya Ministan murna sosai saboda farin cikin da yake da shi wa Ministan.

2 COMMENTS

Leave a Reply