Dan ƙasar China ya kashe budurwarsa ‘yar Kano

2
905

Mr Geng dan kasar china da Ummukulsum Buhari sun yi soyayya,amma daga bisa ni ya sami labarin tayi aure (kamar yadda ya fada).

Dan haka yayi fushi yaje gidan ta ya haura ta taga ya kashe ta a unguwar su dake Jan bulo kuma aka kaita asibitin UMC anan ta rasu.

Hoton ɗakin da yai mata yankan ragon

Ummukulsum ne sunan ta amma an fi kiran ta da Ummita ,ta gama digiri a fannin aikin gona daga jami’ar Kampala dake Uganda yanzu haka tana bautar kasa a Sokoto.

Jami’an immigration da yansanda ne suka kwace shi daga mutanen da suka fara sassama shi a yankin Jan bulo kusa da layin Lawan Kyankyan.

Yanzu haka yana hannun yansanda.

Neptune Prime Hausa na cigaba da bibiyar labarin don sanin gaskiyar lamarin.

2 COMMENTS

Leave a Reply