Da wane dalili ‘yan sanda suka lakaɗa wa ɗan Okada duka a Legas?

Wani ɗan Okada, mai suna Alasan Usman matashi mai ƙoƙarin neman na kansa domin rufawa kansa da ‘yan uwansa asiri.

A ranar jumu’a ‘yan sanda a jihar Legas suka tare shi suka ce ya kawo babur ɗinsa duk da dai bai san laifin da ya aikata ba, sai ya ƙi ya basu. Saboda ya ƙi basu suka masa duka sai kace ɓarawo sai da suka yi masa jina-jina yadda ba zai iya taɓuka komai ba, sannan suka tafi da mashin ɗinsa.

KU KUMA KARANTA: Ranar zuma ta duniya: Amfani da sirrikan dake tattare da zuma

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan Arewa mazauna Legas sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin an baiwa wannan ɗan Okada haƙƙinsa.

Yanzu haka shugaban hukumar ‘yan sanda na jihar Legas ya ziyarce shi a inda yake jinya, sannan an mayar masa da kuɗin belin da aka karɓa na mashin ɗinsa an kuma ba shi guduwmawa mai yawan gaske, kuma yana nan yanzu haka yana samun sauƙi sosai a unguwar Abbatuwa dake Legas.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *