Da gaske ne an fara samun saɓani tsakanin Kwankwaso da Abba?

0
58
Da gaske ne an fara samun saɓani tsakanin Kwankwaso da Abba?

Da gaske ne an fara samun saɓani tsakanin Kwankwaso da Abba?

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rikicin da ke cikin jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano na neman ƙazancewa, inda gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya fara ƙin ɗaga wayar mai gidansa Rabi’u Musa Kwankwaso sannan ya ƙi halartar tarukan da jagoran NNPP ɗin na ƙasa ya shirya.

Da alama dai wannan taken na “Abba tsaya da ƙafar ka” ya fara tasiri a wurin gwamnan bayan da wasu ke ta motsa yadda zai karɓe iko da jam’iyyar da kuma Kwankwasiyya daga hannun Kwankwaso.

Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa tuni Abba ya fara amsa ƙira bayan da “aka nusar da shi cewa Kwankwaso ne ke juya gwamnatin sa inda kusan kashi 90 na makaman da Abba ya yi daga ɓangaren Kwankwaso ne.”

Majiyoyi sun bayyana cewa Abba ba ya jin daɗin “ƙarfa-ƙarfa” da Kwankwaso ya ke yi masa inda ya ya fara nuna alamun ɓoyewa masu ƙira da ya tsaya da kafarsa domin ci gaban sa na siyasa da ma jihar Kano baki ɗaya.

Tun lokacin da aka ga gwamnan a bikin murnar zagayowar haihuwar Kwankwaso, har yanzu ba su sake haɗuwa ba.

KU KUMA KARANTA: Shugabannin mahaifar Ganduje sun koma NNPP

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, majiyoyi sun tabbatar mata cewa duk tarukan da Kwankwaso ya ƙira a Kano da Abuja Abban bai halarta ba.

Majiyoyin sun ƙara da cewa har Abuja Kwankwaso ya bi gwamnan, amma Abba bai bari sun haɗu ba, kuma har ɗan aike ya tura amma Abban ya ƙi ganuwa a wajen Kwankwaso.

Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan majalisar wakilai biyu, Ali Madaki mai wakiltar Dala da Alhassan Rurum mai wakiltar Rano da Kibiya su ka fice daga Kwankwasiyya a ranar Lahadi, wani lamari da ya ƙara fito da riƙon da ke cikin jam’iyyar.

“Yanzu haka ana shirin haɗa kai da wasu ‘yan APC da ‘yan ƙungiyar ‘Abba Tsaya da Ƙafar Ka’ wajen samo umarnin kotu da zai kori dukkan waɗannan ciyamomin da aka rantsar sai a hana CBN da ma’aikatar kuɗi ta hana su kuɗin wata-wata sai dai a baiwa tsagin da Mai Shari’a Simon Amobeda ya tabbatar ana gobe zaɓe,” in ji majiyar.

Sai dai Daily Nigerian ta gaza jin ya bakin Kwankwaso, amma wani na jikin sa ya nuna rashin jin daɗin halayyar da Abba ke nunawa Kwankwason.

Shi ma mai magana da yawun Abba, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ƙi cewa uffan akan batun.

Leave a Reply