Shugabannin mahaifar Ganduje sun koma NNPP

0
56

Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, mahaifar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar zuwa NNPP.

Honorabul Ado Tambai Kwa da taimakinsa, Garba Yahaya Labour, da wasu kansiloli sun sauya sheka zuwa NNPP ne tare da Shugaban Karamar Hukumar Garun-Malam, Mudassiru Aliyu, a ranar Asabar.

Kimanin mako biyu bayan Ganduje, wanda shi ne ya miƙa wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ragamar mulkin jihar ya je jihar inda ya mika wa Abba da jagororin NNPP a Jihar Kano goron gayyata zuwa APC.

Sai dai daga lokacin zuwa yanzu  shugabannin ƙananan hukumomin APC guda uku ne sauya sheƙa zuwa NNPP, a cikin mako guda.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta yaba wa hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamnan Kano

Gwamna Abba ya karɓi Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Auwalu Lawan Aramposu, wanda ya sauya sheƙa zuwa NNPP.

Wannan kuwa na zuwa ne a yayin da wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar masu ci yake karewa ranar 12 ga watan nan na Fabrairu.

Makonni kaɗan bayan ɗan takarar gwamnan Kano na APC kuma tsohon mataimakin Ganduje, Nasiru Yusuf Gawuna ya sha kaye a hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a shari’ar da APC ta ƙalubalanci nasarar Abba.

Da yake karɓar masu sauya sheƙar Gwamna Abba ya yaba da basirarsu ta ganin dacewar su shigo NNPP sannan ya yi musu alƙawarin samun adalci da kuma tafiya tare da su.

Leave a Reply