Daga Ibraheem El-Tafseer
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, da gwamnati ba ta cire tallafin mai ba da wahalar da ake ciki a ƙasar ta fi haka a yanzu.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.
A lokacin jawabinsa na farko bayan rantsuwa, a Abuja, a watan Mayu na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.
KU KUMA KARANTA: Za’a rufe kasuwar canji a Abuja, har sai abin da hali ya yi
Tun daga lokacin da shugaban ya sanar da janye tallafin man kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta ƙara tsada ga jama’a.
Kafin cire tallafin man ana sayar da lita ɗaya a ƙasar a lokacin a kan naira 189 a watan Mayu, amma bayan sanarwar cirewar farashin ya koma daga naira 650 zuwa sama.