Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun yi juyin Mulki a ƙasar Gabon

3
406

Daga Ibraheem El-TAFSEER

Sojoji a ƙasar Gabon, sun fito a gidan Talabijin na ƙasar, inda suka bayyana cewa sun ƙwace mulki. Sun ce sun soke zaɓen da aka yi na ranar Asabar da aka bayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Hukumar zaɓe ta sanar da Mista Bongo a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kashi biyu cikin uku na ƙuri’un da aka kaɗa amma ‘yan adawa sun ce an tafka maguɗi. Wannan matakin ya kawo ƙarshen shekara 53 da aka shafe iyalan gidan Bongo na mulki a ƙasar Gabon.

Sojoji 12 sun bayyana a Talabijin inda suka sanar da soke zaɓen tare da rushe “duk cibiyoyin gwamnati”. Ɗaya daga cikin sojojin ya sanar a gidan Talabijin na Gabon 24 cewa “Mun yanke shawarar tabbatar zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen wannan gwamnatin.”

Mista Bongo ya hau kan mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 2009. Sojojin Gabon sun koka da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da akayi, tare da rusa tsarin mulki.

Wannan ya faru ne a yammacin da akayi zaɓen shugaban ƙasar mai ci, Ali bin Bongo Ondimba a wa’adi na uku da kashi 64% na ƙuri’un da aka kada.

‘Yan adawa sun yi iƙirarin cewa an tabka maguɗi a zaɓen. Iyalan shugaban ƙasar na yanzu sun shafe shekaru 56 suna mulki a ƙasar.Daga 1967 zuwa 2009, shugaban ƙasa shi ne uban shugaban ƙasa na yanzu.

3 COMMENTS

Leave a Reply