Cutar murar tsuntsaye ta ɓulla a Kano

0
22
Cutar murar tsuntsaye ta ɓulla a Kano

Cutar murar tsuntsaye ta ɓulla a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bullar cutar murar tsuntsaye a ƙaramar Hukumar Gwale Jihar Kano.

Sanarwar da Babban Jami’in Lafiyar Dabbobi a Najeriya, ya fitar ta ce cutar murar tsuntsayen tana yaɗuwa ne a tsaka agwagi kaji talo-talo harma da zabbi.

Sanarwar ta na ɗauke da sa hannun Dakta Taiwo Olasoju ta ci gaba da cewa akwai babbar barazanar yaɗuwar cutar murar tsuntsayen daga Kano zuwa wasu sassan Najeriya.

Don haka ya shawarci gwamnatocin jihohi da ofishin lafiyar dabbobin jihohinsu da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace da kuma bin su sau da ƙafa domin daƙile yaɗuwar cutar.

Ya kuma buƙaci a wayar da kan jama’a da nasu kiwo da kasuwancin tsuntsaye kan hatsarin cutar da matakan kariya, sannan hukumomi su riƙa sanya ido sosai tare da kai rahoto idan aka ga wata alama ga hukumomin da suka dace.

Dakta Olasoju ya ce ya kamata a ɗauki matakan ne a Kano da ma faɗin Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji na Jihar Kano, Dakta Usman Gwarzo ya tabbatar da ɓullar cutar da cewa, “a cikin watan Disambar 2024 wani ɗalibin sakandare daga unguwar Galadanci a Ƙaramar Hukumar Gwale ya je Kasuwar Janguza da ke Ƙaramar Hukumar Tofa inda ya sayi agwaga ya kai gida ya sanya a cikin kajinsa sa yake kiwo a kejin katako.

KU KUMA KARANTA: Cutar Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

“Sai agwagwar ta mutu, daga baya kajin suka bi ta, don haka ya kai gawarwakin zuwa asibitin dabbobi dake Gwale inda aka yi gwajin sakamakon ya fito ranar 1 ga watan Janairu, 2025. Amma bayan shi ba a samu makamancin hakan ba a wani gidan kaji kuma a Jihar Kano,” in ji Dakta Gwarzo.

Ya ce ƙungiyar tana aiki da Gwmanatin Jihar Kano domin wayar da kan jama’a da masu kiwon kaji domin kai rahoton duk inda aka ga alamar cutar ko mutuwar kaji da ba a aminta da shi ba.

Leave a Reply