Cire tallafin mai: An tashi baran-baran tsakanin ƙungiyar ƙwadago da Gwamnatin Najeriya

Ganawar da aka yi tsakanin gwamnatin Najeriya da Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasar game da batun janye tallafin mai an tashi baran-baran ba tare da cimma wata matsaya ba.

Nasir Kabiru, Sakataren tsare-tsare na NLC ne ya tabbatar wa BBC hakan inda ya ce ƙungiyarsu sam ba ta amince da tsare-tsaren da gwamnati ta yi ba game da janye tallafin na man fetur ɗin.

A cewarsa, buƙatarsu ita ce a inganta sufuri a kuma yalwata rayuwar ma’aikata kafin a soma aiwatar da tsarin.

KU KUMA KARANTA: NNPC ta ƙara farashin man fetur a Najeriya

An dai shiga tattaunawar ce da ƙarfe 4 na yammacin jiya Laraba a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Ganawar ta samu wakilai daga ɓangaren gwamnati da suka haɗa da Dele Alake, kakakin shugaba Bola Tinubu da kuma shugaban kamfanin mai na ƙasar NNPC, Mele Kyari.

Sauran jami’an gwamnatin sun haɗa da Gwamnan Babban banki, Godwin Emefiele da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

A nata ɓangaren, haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta samu wakilcin shugaban NLC, Joe Ajaero da shugaban TUC, Festus Osifo. A zaman dai an yi ta yamutsa fuska da murza gashin baki, inda ƙarshe, har aka tashi a zaman ba a cimma daidaito ba.


Comments

One response to “Cire tallafin mai: An tashi baran-baran tsakanin ƙungiyar ƙwadago da Gwamnatin Najeriya”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Cire tallafin mai: An tashi baran-baran tsakanin ƙungiyar ƙwadago da Gwamnatin Najeriya […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *