Cikin watan Fabrairu za’a fara tonon man fetur da ke Bauchi – Mele Kyari

0
77

Daga Maryam Umar Abdullahi

A watan Fabrairun da mu ke ciki ne ake sa ran za a fara tonon albarkatun man fetur da iskar gas da aka samu a Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Bauchi ta kudu, Sanata Shehu Buba ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon sashen Hausa na Muryar Amurka a Bauchi.

KU KUMA KARANTA:Sarki Charles III na Ingila, yana fama da cutar kansa

Yace Manajan Darektan kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ne ya shaida masa da mai ba da shawara kan sha’anin tsaro na ƙasa, Malam Nuhu Ribadu yayin da suka ziyarci ofishin kamfanin a Abuja.

A cewarsa, Manajan Daraktan ya ba da tabbacin cewa kamfanin da aka baiwa aikin haƙar albarkatun man fetur ɗin daga ƙasar Indiya ya iso Najeriya don fara
aiki gadan-gadan a cikin wannan watan na Fabrairu.

Leave a Reply