CEFFTAIWA ta shirya wa lauyoyi da ‘yan jarida taron ƙara wa juna sani a Kaduna

0
52
CEFFTAIWA ta shirya wa lauyoyi da 'yan jarida taron ƙara wa juna sani a Kaduna

CEFFTAIWA ta shirya wa lauyoyi da ‘yan jarida taron ƙara wa juna sani a Kaduna

Daga Idris Umar, Zariya

Cibiyar kula da bin ƙa’idar kuɗaɗe ‘Center for Fiscal Transparency and Integrity Watch,” ta shirya taro don ƙarawa juna sani ga ‘yan jaridu da lauyoyi a kan bin ƙa’ida da cikakkiyar kulawa da kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Yayin da ya ke magana a wajen taron babban daraktan cibiyar, Umar Yakubu, ya ce haɗa manema labarun da lauyoyin a wuri ɗaya domin a iya samun wata hanya ne domin yin bincike ga kuɗaɗen da ake ware wa ƙananan hukumomi daga ma’ajiyar ƙasa.

Umar ya ce ‘yan jaridan da lauyoyin suna a matsayin da ya dace domin yaƙi da cin hanci ta hanyar yin aikin jaridar da ya shafi bincike, a yayin da su kuma lauyoyin za su bi tanade-tanaden doka domin yaƙi da cin hancin.

Kamar yadda babban daraktan ya bayyana, a yayin da ake da cikakkiyar kulawa tare da bin ƙa’ida, cin hanci zai ragu.

Yakubu ya ce yana fa ta ya ga canje-canje daga masu riƙe da ofishin siyasa dangane da cikakkiyar kula, musamman a yankunan ƙananan hukumomi, waɗanda sune ke kusa da mutane.

Babban daraktan ya bayyana damuwarsa a kan rashin mayar da hankali daga ƙananan hukumomi wajen samar da bayanansu a shafinsu domin a iya samun bayanan cikin sauki.

Shi ma yayin da ya ke jawabinsa, Barrister A.Y Musa, lauya daga Zariya, ya bayyana taron karawa juna sanin da wanda ya fita daban kuma wanda ya zo a kan lokaci domin amfaninsa.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar lauyoyi ta bayyana damuwa kan tauye ‘yancin ba da kariya

Barrister Musa ya ce akwai abubuwa da dama da ke shafar aikin lauyoyi yayin da suke aiki a kan shari’ar da ta shafi cin hanci, musamman da ya shafi masu ruke da mukaman siyasa.

Ya bayar da shawarar da su ci gaba da shiraya irin wannan tarukan tare da gayyato jami’ai daga ICPC da EFCC don samun ƙwarin gwiwar sanin wasu ilimi a ɓangarensu.

Da ya ke bayar da na sa gudummuwar, Abubakar Sadiq Mohammed, wanda ya ke ɗan jarida, ne a kafar yaɗa labarai na Daily Trust Shi ma ya yi addu’ar cewa irin wannan taro bai kamata a tsaya hakaba ya dace a ci gaba ƙirkiro hanyar ci gaban taron saboda muhimmancin sa kuma yayi fatan dukkan mahalarta taron za suyi amfani da abin da aka tattauna a wajan taron.

Bayan kammala taron anyi zaman kulla zumunta tsakanin lauyoyin shiryar Zariya da kungiyar NUJ shiyyar Zariya don bunkasa aikin juna da yiwa ƙasa hidima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here