CBN ta saduda, ta umurci bankuna da su karɓi N500 da N1000

Sa’o’i 24 bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dawo da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 a kasuwa, wanda hakan ya zama doka daga ranar 10 ga Fabrairu, 2023 zuwa 10 ga Afrilu, 2023, babban bankin ya umarci sauran bankuna da su karɓi tsohon N500 da N1,000 daga kwastomomi, kamar yadda wani babban jami’in bankin koli ya bayyana.

Hakan na zuwa ne bayan sanarwar farko cewa kwastomomin su zarce zuwa ofisoshin babban bankin ƙasar nan don ajiye tsofaffin takardun kudi – N500 da N1,000. Ana kyautata zaton cewa sabon umarnin na da nufin sauƙaƙa wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta waɗanda har yanzu basu gama kai tsofaffin takardun kuɗinsu ofisoshin bankin koli ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano zata rufe duk gurin da ba a karɓar tsohon kuɗi

Wani babban jami’in banki kuma shugaban reshen, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa reshen zai karɓi tsofaffin takardun kuɗi daga hannun abokan hulɗa a gobe Asabar saboda reshen bai buɗe wa kwastomomi a yau ba, saboda fargabar kai hari.

Idan mai karatu zai tuna, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin cewa tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1,000 sun haramta a hada hada da cinikayya, amma waɗanda ke da takardun su kai wa babban bankin ƙasa CBN domin kada su yi asarar kuɗaɗen su.

Neptune Prime ta ruwaito cewa CBN ya bude portal ga mutanen da ke da tsofaffin N500 da N1,000 don yin rajistar nawa suke son sakawa da kuma samun lambar tantancewa don tabbatar da rajistar a can.

Za a yi amfani da lambar tantancewa wajen ajiye tsofaffin takardun a kowane ofisoshi na CBN dake faɗin kasar nan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *