Burinmu Shi Ne Samar Da Tsaro Da Fahimtar Juna Tsakanin Al’umma A Najeriya – Dakta Peterx

1
366

Daga; Abdullahi Alhassan, Kaduna.

Dakta Maji Peterx, shi ne Babban Daraktan a Kungiyar mai yunkurin wazan da zaman lafiya a tsakanin Al’ummomin daban daban a Najeriya, mai Suna Equil Access lntetnational (EAI), dake aikin tabbatar da kare al’ummar Najeriya da ma samar da fahimtar juna, musamman a jahohin a kasar nan, da suka hada da Benue, Filato, Kaduna da Kano.

Da yake jawabi a wajen wani taron da suka kira a Kaduna tare haɗin gwiwa Gidauniyar wanzar da zaman lafiya ta CLEEN Foundation, Mai taken “Kare Al’ummar Najeriya”dake gudana a garin Kaduna, Dakta Peterx ya bayyana cewa fatan su shi ne ganin an kare afkuwar tashin hankalin, ana samu fahimtar juna tsakanin al’ummomi daban -daban dake rayuwa a Najeriya.

Acewarsa, wannan yasa suka kira wannan taro da ya hada da Shugabannin Kungiyoyin Matasa, Jami’an tsaro, Sarakuna, Shugabannin Addinai, da suka hada da JNI, CAN, Mata da Masu bukata ta musamman wato nakasassu, don ganin an tattauna hanyoyin da za a bi na dakile tashin hankalin a yankunan su.

Ya kara da cewar manufar wannan taron shi ne saka Jami’an tsaro, Shugabanin Al’umma, Mata da Matasa, dake Kaduna don ganin an cimma hanyoyin Kare al’ummar Najeriya, domin wannan ne ma taken taron, saboda samar da zaman lafiya a yankunan dake fama da matsalar tsaro da rikece-rikice, don kawo karshen ta a yankunan da suka fito dama Najeriya baki daya.

Ya ce “Wannan taron zai bude Kofar fahimtar juna tsakanin Al’ummomin, ta hanyar da kowa zai zama mai hannu da shuni ko mai ruwa da tsaki kan harkar tsaro, muna fatan abinda aka tattauna a nan kowani Mutum wakilin Al’ummar su ne kuma zai koma gida ya fadakar da su kan wannan aiki da suka sa a gaba na kare afkuwar tashin hankali a kasar nan.”

Shi kuwa Jami’in Shirye-Shirye na Gidauniyar ta CLEEN Foundation, Mista Ebere Mbeagbu, ya bayyana cewa taron zai fadakar da Jami’an tsaro, da Shugabannin al’umma kan yarda zasu kare afkuwar tashin hankali a cikin yankunan su, tare kuma da hanyoyin dakile faruwar tashin hankalin kuma zai basu dama ta hanyar da za subi na ganin cewa sun bada gudunmawa cikin harkokin samar da zaman lafiya.

Mista Ebere Mbeagbu, ya kara da cewar irin wannan zai magance rashin fahimta tsakanin Jami’an tsaro da Mutanen gari, haka kuma zai sa mutanen su ji cewar suna da rawa da zasu taka kan samar da tsaro kasancewar shi tsaro abu ne dake da bukatar sa hannun kowa.

“Muna fatan cewar a karshen wannan taron ya zama cewar mahalarta taron sun koyi abubuwan da zasu habbbaka aiyukan da muka sa gaba na Kare Al’ummar Najeriya, haka kuma farfaɗo da zaman lafiya a tsakanin Al’ummomin daban-daban da ke rayuwa a Najeriya.

A nashi Jawabin yayin wannan taron Mista Samuel Aruwan, wanda shi ne Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na Jahar Kaduna, kira ya yi da al’umma da su rika kai rahoton duk wani abu da basu amincewa ba ga Jami’an tsaro don ɗaukar matakan kariya daga Jami’an tsaron.

Inda ya kara da cewar Gwamnati a shirye take na ganin ta kare rayuka da kuma dokiyuyin Al’umma don haka akwai bukatar sanar da Jami’an tsaro duk halin da aka ganin na tashin tashina ne don kawo musu daukin gaggawa.

Mista Aruwan ya ce “muna cikin wani mawuyacin hali na matsalar tsaro saboda haka, Jami’an tsaron mu baza su lya karade duk ko wani sakuna da lunguna na fadin wannan Jahar ba, saboda haka dole ne Al’umma ltama ta bada gudunmawa ta hanyar bawa Jami’an tsaro bayanai da zamu taimaka musu akan aikin su.

Ya kuma ce zamu lya magance rashin hankali da kuma kalubalen tsaro ldan muka hada hannu wajen yin aiki tare, ta hanyar sanar da Jami’an tsaro, Gwamnatin Jahar Kaduna a shirye take na ganin ta karbi duk wani abu da zai kawo mana zaman lafiya a Jahar mu.

Su kuwa mahalarta wannan taron cewa su ka yi taron yazo kan lokacin da ya kamata, kuma zai kawo karshen rikici da taimakawa wanzuwar zaman lafiya da ma fahimtar Juna a Jahar.

Imam Shafiu Hassan, wani Malamin addini daga karamar hukumar Kajuru, ya ce shi yanzu Jakadan zaman lafiya ne, haka kuma sun rungume zaman lafiya a yankunan su.

Shima Mista Titus Dauda wanda shi ne Dagacin kufana a karamar hukumar Kajuru, ya bayyana cewa taron bitar zai basu damar sanin hanyoyin da zasu bi na magance rikici a yankin su, ta hanyar hada kai da Jami’an tsaro na ganin cewa sun kare rayuka da duniyoyin al’ummar su.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here