Buhari har kulle ɗakinsa yake yi, saboda ya yarda da jita-jitar cewa zan kashe shi — Aisha Buhari
Aisha Buhari, matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ta ce mijinta ya fara kulle ɗakinsa bayan jita-jitar da ta bazu a Aso Rock cewa tana shirin kashe shi.
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce Buhari ya yarda da abin da ake yadawa, lamarin da ya sa ya sauya wasu daga cikin halayensa.
Aisha ta bayyana ƙwarewarta wajen kula da matsalolin lafiyar Buhari a cikin wani littafin tarihin rayuwarsa mai shafuka 600 mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari” (Daga Soja zuwa Jagoran Ƙasa: Tarihin Muhammadu Buhari).
KU KUMA KARANTA: Aisha Buhari Ta Gayyaci ‘Yan Takarar Shugaban kasa Shan Ruwa Da Sharadin Banda Zuwa Da Waya
A cikin littafin, Aisha ta ce matsalar lafiyar da Buhari ya fuskanta a shekarar 2017 ba wata cuta ce mai ban mamaki ba ko sakamakon guba, sai dai ta fara ne bayan rushewar tsarin cin abinci da kuma rashin kula da tsarin gina jiki yadda ya kamata.
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce tun da dadewa ita ke kula da abincin mijinta a wasu lokuta na musamman, tana mai cewa tsarin ya taimaka wa Buhari wajen kiyaye daidaiton lafiyarsa.
“A cewar Aisha Buhari, matsalar lafiyar mijinta ta shekarar 2017 ba ta samo asali daga wata cuta mai ban mamaki ko makirci na ɓoye ba. Ta fara ne da lalacewar tsarin rayuwa; abin da ta kira ‘tsarin abincina’—wato tsarin cin abinci da ƙarin gina jiki da ta dade tana kula da su a Kaduna kafin su koma Aso Villa,” in ji littafin.









