Budurwa tayi awon gaba da motar saurayinta a Kano, lokacin da ya fita Sayen Shawarma

0
357

Daga Shafaatu Dauda, Kano

An kama wata budurwa da ta sace motar saurayinta ta gudu bayan ya fita sayo mata Shawarma a unguwar ƙofar Famfo, da ke kan titin Jami’ar Bayero a Birnin Kano.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar wa manema labarai cewa, wanda aka ɗauke wa motar a ranar 12 ga Yulin 2022, ya kai ƙorafin cewa an sace masa mota.

Bayan da ’yan sandan suka kama budurwar mai suna Ilham, ta bayyana cewa tana bin saurayin nata kudi ne N150,000 kuma tana ganin ba zai ba ta ba, shi ya sa ta yanke shawarar dauke masa mota.

Sai dai a cewar saurayin, sun yi waya ne kuma suka hadu a hauren wanki, inda daga nan ta ce tana jin yunwa kuma Shawarma take son ci.

Sai dai fitarsa ke da wuya domin siyo mata shawarmar ya dawo ya tarar da motar ta yi batan-dabo.

Ilham dai ta bayyana wa ’yan sanda cewa wani saurayinta ta kirawo ya tuƙa motar ya tafi da ita gida ya ajiye mata kuma ta ɗauki motar ne domin kudin da take bin saurayin.

Tuni dai aka kama ta da saurayin nata da ya tuka motar domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply