Daga cikin abubuwa masu ban a’ajibi a hallittun tsirrai, shi ne wata bishiyar fure da aka bai wa sunan “Zuciya mai zubar da jini,” wadda ake amfani da kyawunta wajen bayyana yanayin halayyar ɗan’adam da ba a buƙata.
A yayin da wannan bishiya ba ta zubar da jini a zahiri, hotuna da bidiyo a faɗin duniya na nuna yadda wasu bishiyoyi suke fitar da wani jan ruwa kamar jini, abun da ke ci gaba da tayar da hazo kan fassararsa a gargajiyance da kimiyyance a tsakanin al’ummu.
A yankuna irin su Kudancin Amurka, ana kuskuren kallon wannan ruwa a matsayin jini, yayin da a Afirka, abin da aka fi imani da shi shi ne wai wasu mutanen ɓoye ne da ke rayuwa a cikin bishiyoyin ke fitar da jan ruwan.
A watan Oktoban 2017, masanin tsirrai ɗan ƙasar Faransa ya bayar da haske kan yadda Tepezcohuite ko “bishiya mai aman jini”, ta zama abar girmamawa a wajen jama’ar Mayas da ke kudanci Mexico zuwa Guatemala.
Wani bidiyo da aka yaɗa a yanar gizo ya tabbatar da wanzuwar irin waɗannan bishiyoyi masu zubar da ruwa kamar jini. Mene ne abin da ake muhawara a kai game da wannan jan ruwa da ke bulbulowa?
KU KUMA KARANTA: Abubuwan al’ajabi da ke tattare da dabbar ‘Batoyi’ (Hotuna)
Kimiyya ta yi watsi da wannan abi bisa cewa camfi ne kawai idan aka ce wai wannan ruwa d abishiyun ke fitarwa jini ne. Amma jama’ar Shaman da masu bin addinan gargajiya na yi wa wadannan bishiyu kallon masu tsarki.
Dr Djibril Diop, masanin muhalli kuma malami a Jami’ar Cheikh Anta Diop da ke Dakar babban birnin Senegal, ya bayyana cewa babu wata bishiya da ke aman jini ko take da wani ikon amfanarwa ko cutarwa saboda jan ruwan da take da fitarwa.
Ya nanata cewa wannan ruwa wani ɗanko ne ko ruwan cikin tsirrai danda ke taka muhimmiyar rawa wajen rayuwarsu.
Ɗankon cikin tsirrai wani ruwa ne da ke fita daga bishiya don tsaron kanta, inda ruwan cikin jijiyoyin bishiya kuma yake kasancewa fari, kuma yana fita da tsakanin gajye da reshe, wanda shi ke kai ruwa, gishiri, ko sukari ga tsirrai.
Dr Diop ya bayar da misali da bishiyar darbejiya a yankin Bandafassi take fitar da wani farin ruwa mai yawa saboda harin ciwon fungal.
“Mazauna yankin na fassara wannan da wani abin a’ajibi kan bishiyar, ba tare da sun san cewa yanayin bishiyar, yankin da take, ƙasar data fito daga ciki da kuma yanayin ciwon da za ta yi na taka rawa wajen fitar ruwan da kalarsa.
Masanin muhallin ya kuma yi nuni da cewa babu wata bishiya da ke da jini, a saboda haka a hankalce, ba za a taɓa tsammanin ta fitar da jini ba.
Ya bayar da misali da bishiyar da ake ƙira Socotra don nuni ga yadda ɗanko a reshan bishiya yake, tare da kalar jan da wasu ke tunanin ko jini ne.
Wannan bishiya da za ta iya tsayin har mita 20, na fitar da ruwa ja daya sanya har aka rubuta wasu makalolin kimiyya don bayyana ta a matsayin “bishiya mai aman jini”.
Wannan jan ruwa ya haɗa da sukari, ruwa da wasu sinadaran gina jiki, kuma a wasu al’adu ana amfani da shi wajen rini. Ana yawan alaƙanta wannan ruwa ja ga ƙarfin tace sinadarai da bishiya ke yi.
Baya ga amfani da su wajen yin rini, masana tsirrai irin su Dr Diop da masu maganin gargajiya irin su Romaric Moussounde Moussounda na da ra’ayin cewa wadannan bishiyoyi na yin magani.
Moussounda, wanda ke da fahimta kan bambance-bambancen dazukan Gabon, na da ra’ayin cewa halittu da yawa, ko nau’ikan bishiyoyi Pterocarpusda ke Afirka ko na Abitibi da ke Quebec, duk sun cancanci a yi musu kallon masu matsayi na musamman ko yin camfi game da su.
Moussounda ya na cewa “Waɗannan bishiyoyi kyauta ce daga Ubangiji da bai kamata su faɗa wani rukunin rashin tabbas ba.”
“Wannan ruwa da ke fitowa daga cikin waɗannan bishiyoyi na jini ba ne, amma kuma na da muhimmanci da matsayi irin na jini.”
Moussounda wanda ke cakuɗa gargajiyanci da zamananci a fannin kula da lafiyar zuciya da sauran ayyukan gaggawa na kula da lafiya, ya rawaito marubuci dan asalin Senegal Birago Diop, wanda a 1960 ya yi rubutu game da “Tsarkin wasu bishiyoyi”.
Moussounda ya ce “Ana yawan amfani da waɗannan bishiyu masu tsarki wajen bukukuwa da magani. Duk suna da wata alaƙa ruhaniyya ga ɗan adam.”
A yayin da masana tsirrai ke ta fashin baki kan waɗannan bishiyu masu aman jini, su kuma mabiya addinan gargajiya irin su Mayan da ke Mexico da ‘yan asalin Indiya na Barazil ko Kudancin Amurka na da ra’ayin lallai a kalli waɗannan bishiyoyi a matsayin masu tsarki ababan girmamawa.
Duk da waɗannan bambance-bambance na ra’ayi, akwai ijma’i tsakanin masana kan lallai a kare wadannan bishiyoyi, ko suna da tsarki ko babu, don kare muhalli.