Daga Ibraheem El-Tafseer
An fara fuskantar ƙarancin Ayaba a manyan kantunan Birtaniya saboda matsalolin sauyin yanayi da ke tarnaƙi ga samar da Ayabar.
Ƙwararru sun ce masu son cin Ayaba na fama da tsadarta sakamakon yadda sauyin yanayi ke tasiri kan nomanta a sassan duniya.
Wani mai sharhi kan sha’anin tattalin arziƙin Ayaba a Majalisar Ɗinkin Duniya, Pascal Liu, ya shaida wa BBC sauyin yanayi na janyo tsaiko da yaɗa cututtukan da ke lalata amfanin gona.
KU KUMA KARANTA : Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai
Tun a makon da ya wuce ake fuskantar ƙaranci ko rashin Ayabar a wasu kantina na ƙasar, bayan guguwar da ta faɗa a tekun Atlantika da ta janyo tsaikon dakon Ayabar ta jirgin ruwa.
Ƙwararru za su yi taro a birnin Rom, domin tattaunawa kan wannan matsala ta ɗaya daga cikin abin da aka fi ciniki da kawo bunƙasar tattalin arziƙi.