Ban mamaki: Ɓarayi sunyi satar makudan kuɗi a gidan Gwamnatin Jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da labarin satar kuɗi maƙudai da wasu da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka yi a ma’adanar kuɗi ta gidan gwamnatin jihar.

Darakta Janar na Gwamna Masari mai kula da kafafen sadarwar zamani Mal Al’amin Isah ne ya tabbatar da labarin, ga manema labarai, sai dai ya ce ba zai iya fadin ko nawa ne aka sace ba.

Majiyar Blueink ta rawaito cewa Mal Al’amin Isah ya ce tuni an kama wasu da ake zargi, su na ma tsare a hannun ‘yan sanda ana bincikensu.

Sai dai akwai raɗe-radin da ke yawo cewa kuɗin sun kai Naira milyan 31.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *