Bagudu ya halacci taron bunƙasa harkar noma a Abuja

0
120

Daga Idris Umar, Zariya

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi na ƙasa a ranar Talata 16/04/2024, Ya halarci wani shiri na musamman a babban birnin tarayya Abuja domin bunƙasa sha’anin harkokin ayukkan gona a faɗin Najeriya.

Shirin wanda yake ƙarƙashin gwamnatin ƙasar Jamus (Germany ) da kuma ƙungiyar GIZ zai bayar da gagarumar gudumuwa wajen bunƙasa sha’anin ayukkan gona a Najeriya.

Bagudu ya bayyana alfanun da ke akwai ta haɗaka da ƙungiyoyi ire-irensu GIZ ta hanyar musayar ilmi da amfani da zamani wajen cimma manufa, Bagudu ya ƙarfafawa mutanen da suka halarci shirin da su rinƙa shirya taron ƙara wa juna sani domin cimma kyakkyawar manufar ciyar da ƙasa gaba.

KU KUMA KARANTA: Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano

Bagudu ya ƙara fayyace cewar haɗaka na da matuƙar muhimmanci domin ta hakan ne za’a samu ci gaba a fannin tattalin arziƙi da ci gaba a Najeriya.

Leave a Reply