Bada Tallafi: Kansilan Gargari Ya Yabawa Ahmed Abbas

0
459

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

KANSILAN Mazabar Gargari Malam Abdulahi Yahaya Dungurawa ya jinjinawa mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Kano kan harkokin cikin gida malam Ahmed Abbas Ladan bisa kokarin da ya yi na bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa domin samar da dogaro dakai.

Ya yi wannan yabon ne jim kadan bayan kammala bikin bada tallafin wanda ya gudana a makarantar sakandire ta Dawanau bisa jagodancin Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.

Malam Abdulahi Yahaya Dungurawa ya kuma bayyana wannan tallafi a matsayin wata hanya ta bunkasa harkokin zamantakewar al’umma maza da mata musamman a daidai wannan lokaci da ake ciki na bukatar samun karin hanyoyi na kyautata rayuwa kamar yadda ake kokari.

Haka kuma kansilan na mazabar Gargari ya godewa Uwar-gidan Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje saboda kokari da take yi wajen halartar dukkanin wata hidima ta al’umma a fadin Jihar Kano, wanda hakan ya tabbatar da cewa tana son ganin kowa yana cikin yanayi mai kyau.

A karshe, Malam Abdulahi Yahaya Dungurawa ya yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa da mataimakin sa Garba Yahaya Labour da daukacin kansiloli zababbu da nadaddu da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki kan harkokin tafiyar da jagorancin wannan yanki.

Leave a Reply