Kotu Ta Aika Da Dan Bilki Kwamanda Gidan Gyaran Hali A Kano

0
295

Daga, Rabo Haladu.

WATA kotu a Kano ta aika da Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan gyaran hali.

Dan Bilki zai cigaba da zama a gidan yarin har zuwa 15 ga watan Maris.

Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Dan Bilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.

Ana tuhumarsa da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.

Leave a Reply