Babu wani gyara da El-Rufai ya yiwa manyan asibitocin jihar Kaduna – Uba Sani

0
207

Gwamna Uba Sani na Kaduna ya bayyana cewa babu wani gyara da aka yi wa manyan asibitocin jihar guda 32 cikin shekaru 20 da suka gabata.

Da yake jawabi a gidan Gwamnati da ke Kaduna a ranar Alhamis, Uba Sani ya yi jawabi ga taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga dukkanin ƙananan hukumomi 23 da suka zo masa Barka Sallah.

Ya jaddada cewa an tilastawa mazauna yankin neman magani a jihohin da ke maƙwabtaka da su saboda rashin asibitocin dake aiki a Kaduna.

Gwamnan ya sha alwashin Gwamnatin sa na ganin ta gyara, sake ginawa da kuma inganta manyan asibitoci guda shida, inda asibitoci biyu za su kasance a kowane shiyyar da ke jihar nan ta majalisar dattawa.

KU KUMA KARANTA: El-Rufai ya bar wa jihar Kaduna ɗimbim bashi – Gwamnan Uba Sani

Ya ƙara da cewa, “Wannan aiki da yardar Allah za a fara shi ne a ranar Litinin mai zuwa, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, saka hannun jari a fannin kiwon lafiya, musamman a matakin kula da lafiya na sakandare ya zama wajibi, galibin waɗannan asibitocin an yi watsi da su tun shekaru 20 da suka gabata.

Leave a Reply