Babbar Mota ta ƙwace ta kashe mutane a Anambara

Wani direban babbar mota da ya ke gudun wuce ƙa’ida, a ranar Talata ya kashe wani mutum da ke tafiya a kan hanya a mahaɗar Immigration da ke kan titin Awka zuwa Onitsha, Anambra.

Adeoye Irelewuyi, babban kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya, (FRSC) a jihar, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar lamarin a Awka.

Mista Irelewuyi ya ce hatsarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 8:15 na safe, ya faru ne sakamakon gudun wuce ƙa’ida da kuma rashin kula.

“Hatsarin ya rutsa da wani direban babbar motar kasuwanci da ba a tantance ko wanene ba mai lambar jikin mutum: OPL-1A-022 mallakar Dangote.

“Wanda da abin ya faru a kan idonsa ya nuna cewa direban motar da ke cikin gudu ya kutsa kan wani mai tafiya a ƙasa inda ya murƙushe shi nan take.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 14, ya jikkata 5 a Bauchi

“Maza uku ne hatsarin ya rutsa dasu. An kashe ɗaya daga cikinsu, yayin da aka ceto sauran biyun ba tare da jikkata ba.

“Rundunar ceto ta FRSC ta garzaya da mamacin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Chukwuemeka Odimegwu Ojukwu da ke Amaku, Awka, inda aka tabbatar da mutuwarsa, kuma an ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawawwaki na Asibitin,” inji shi.

Ya ce, direban babbar motar da ya yi ƙoƙarin tserewa wani Bamasare ne ya tare shi, lamarin da ya sa aka kama shi, inda ya ce tuni aka miƙa shi ga ‘yan sanda domin ci gaba da ɗaukar mataki.

“An ja motar zuwa sashin ‘B’ na ‘yan sandan Najeriya da ke Awka,” inji shi. Kwamandan ya jajantawa iyalan mamacin, ya kuma gargaɗi masu ababen hawa da su guji yin gudu tare da shawarce su da su kiyaye ƙa’ida.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *