Babban Bankin Najeriya ya soke lasisi 4,173 na masu canjin kuɗin ƙasashen waje

0
255

Babban Bankin Najeriya, CBN, ya soke lasisi 4,173 na masu canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da ba su cika wasu sharuɗɗa da ya gindaya musu ba.

CBN ya bayyana haka ne a wata sanara da ya fitar ranar Juma’a da maraice mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun bakin Hakama Sidi Ali.

Sanarwar ta ce sharuɗɗan da ƴan kasuwar canjin kuɗin suka gaza cikawa sun haɗa da “rashin biyan haraji, ciki har da ƙin sabunta lasisi” da “ƙin bin dokokin CBN, musamman waɗanda suka shafi yaƙi da masu halatta kuɗaɗen haramun da ƴan ta’adda.”

A farkon makon nan ne CBN ya koma sayar da dala ga wasu ƴan kasuwar canjin kuɗin ƙasashen waje a yunƙurinsa na rage hauhawar da farashin dala ke yi, lamarin da ke yin mummunan tasiri kan tattalin arzikin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin 100

Kazalika jami’an tsaron Najeriya sun tsare biyu daga cikin shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto wato Binance waɗanda ake zargi suna haddasa tashin farashin dala a ƙasar.

Ranar Talatar da ta wuce, gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya ce wasu mutane da ba su sani ba “sun yi hada-hadar dala biliyan 26 ta manhajar Binance a Nijeriya a cikin shekara ɗaya da ta wuce”.

Leave a Reply