Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kaso 27.5 cikin 100

0
13
Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kaso 27.5 cikin 100

Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kaso 27.5 cikin 100

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara yawan kuɗin ruwa a kan basussuka (MPR)daga kaso 27. 25 zuwa kaso 27.50 cikin 100 a wani yunƙuri na yaƙi da hauhawar farashin kayan masarufi.

Hakan ya biyo bayan taron kwamitin manufofin kudi (MPC) na babban bankin Najeriyar.

Da ma’aunin MPR ake auna araha ko tsadar bashi.

KU KUMA KARANTA: Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin 100

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso ne ya sanar da hakan a Abuja a jiya Talata yayin taron kwamitin manufofin kudin bankin na karshe a bana da ya gudana a shelkwatar babban bankin.

Cardoso yace gaba-dayan mambobin kwamitin na MPC ne suka amince da kara kudin ruwa da maki 25 daga kaso 27.25 zuwa kaso 27.50 cikin 100, tare da barin adadin tsabar kudi a kan kaso 50 cikin 100 ga bankunan ajiya da kaso 16 cikin 100 ga bankunan hannayen jari.

Wannan shine karo na 6 da CBN ke kara yawan kudin ruwan tun cikin watan Fabrairun 2024.

A watan Satumba, bankin ya ƙara kuɗin ruwan zuwa kaso 27.25 cikin 100 sakamakon raguwar da hauhawar farashin kayayyaki ta yi a watan Agustan 2024.

Leave a Reply