Ba zan yi wa kowa takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba — Obi

0
64
Ba zan yi wa kowa takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba — Obi

Ba zan yi wa kowa takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba — Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2027, Peter Obi, ya ce ba shi da sha’awar zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga kowa a zaɓen 2027.

Daily Trust ta rawaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a yau Asabar a shafin sa na X.

A cewarsa, an yi wa wasu kalamai da ya yi yayin ganawa da News Central TV gurguwar fahimta.

Obi ya ce a yayin tattaunawar, ya yi amfani da damar wajen yin bayani kan matsayar sa dalla-dalla, amma wasu mutanen suka dinga yada akasin hakan.

KU KUMA KARANTA:Rashin iya lissafi ne ya sa wasu suke cewa an yi cushe a kasafin kuɗin 2024 – Tinubu

“Domin kaucewa ruɗani, ni ban ce zan zama mataimakin shugaban ƙasa ba”.

”Na sha faɗa cewa, a shirye nake nayi aiki da wadanda ke son gina sabuwar Nijeriya.

“Bana son zama irin mutanen dake ta ɓaɓatu kan batun 2027 a yayin da ‘yan Nijeriya ke fama da yunwa da matsalar tsaro da sauran kalubale”, inji Obi.

Leave a Reply