Ba zan yi amfani da kuɗin talakawa wajen neman tazarce ba – Abdullahi Sule

1
501

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bada tabbacin cewa ba zai yi amfani da kobo ɗaya daga dukiyar jihar wajen yakin neman zaɓe a zaɓen 2023 ba.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake jawabi a matsayin babban ɓako a wajen taron Karatun Ƙur’ani na kasa tare da bayar da tallafin kuɗi da ƙungiyar masu Karatun Ƙur’ani ta Najeriya ta shirya a ranar Lahadi.

“Ba zan yi amfani da dukiyar jihar nan wajen neman tazarce ko wani wa’adin mulki ba.

Ya bayyana cewa domin a samu saukin yaƙin neman zaɓensa, abokansa, abokan aikinsa da shugabannin da ya yi aiki da su a lokacin da yake sana’o’i ne suka haɗa masa kayan aiki a kwanan baya a wani ƙudiri da aka yi a Abuja, inda aka samu sama kuɗi Naira biliyan ɗaya da naira miliyan 200.

KU KUMA KARANTA ‘Yan sandan Kano sun kama mutum 7 da mallakar katin zaɓe ba bisa ƙa’ida ba

Yayin da yake jawabi a kan mimbari tare da kawo ayar Al Ƙur’ani mai tsarki, gwamnan Sule ya yi magana kan buƙatar ‘yan siyasa masu neman mulki suyi taka tsan-tsan don kada su zafafa harkokin siyasa.

“Allah yana ba da mulki ga wanda ya so, kuma a lokacin da yazo, kamar yadda ya bayyana a cikin Alkur’ani mai tsarki”

Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen yin jawabi a kan buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen magance matsalar barace barace a kan tituna.

Ya ce akwai banbanci tsakanin mai bara da Almajiri, wanda shi mai neman ilimi ne, ya ce gwamnonin Arewa sun damu matuƙa kan yadda wasu iyaye ke tura ‘ya’yansu zuwa wurare masu nisa, galibi a faɗin jihohi, ba tare da sun yi shiri don kula da su ba, kuma yaron ba shi da wani abin da zai yi sai dai tsira ta hanyar bara.

“Babu wanda zai iya hana musulmi ‘yancin samun ilimi, sai dai iyaye su daina tura ‘ya’yansu ba tare da sun shirya biyan buƙatunsu na yau da kullun ba.

Gwamnan ya bada gudunmuwar naira miliyan goma sha uku domin gudanar da wannan asusu, sannan ya bayar da tallafin motoci guda biyu, ɗaya na ƙungiyar reshen jiha da na ƙungiyar a mataki na ƙasa.

1 COMMENT

Leave a Reply