Daga Ibraheem El-Tafseer
Faransa ta musanta zargin karya dokar sararin samaniya da sojojin mulki a Nijar suka zarge ta da yi.
Sojin Nijar sun zargi Faransa da karya dokar ƙasar ta rufe sararin samaniyarta.
Sojojin Nijar sun zargi Faransa da ƙawayenta da ƙoƙarin kuɓutar da ‘yan ta’adda da ke tsare, waɗanda ake zargi da haifar da rashin tsaro tsawon shekaru takwas.
Amadou Abdraman ne ya bayyana zargin cikin wata sanarwa da ya karanta a talabijin, sai dai babu wata shaidar da ya gabatar game da zargin.
Hakan na zuwa ne lokacin da ake zaman ɗar-ɗar kan zaman da ƙungiyar Ecowas za ta yi a gobe Alhamis, inda za ta tattauna matakan da za ta ɗauka nan gaba, ciki har da matakin soji.
KU KUMA KARANTA: Nijar ‘yan’uwanmu ne, kar a tura sojoji su yaƙe su – El-Zakzaky ga Tinubu
Gwamnatin Faransa ta musanta zargin na sojojin Nijar kan kuɓutar da “yan ta’adda” da kuma karya dokar keta sararin samaniyarta.
Lamarin na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da wani tsohon jagoran ‘yan tawaye ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.
Yau Laraba ma an kama ɗan jakadiyar Nijar a Faransa, Idrissa Kané, wadda tsohuwar shugabar gidan waya ne na Nijar, inda ake zargin sa da almubazzaranci da dukiyar al’umma.










[…] KU KUMA KARANTA: Ba mu kai wa jamhuriyar Nijar hari ba – Faransa […]