Dokta Chris Ngige, Ministan Kwadago da Aiki, ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan yadda ya raina shugaba Muhammadu Buhari a sakonsa ga ‘yan Najeriya na sabuwar shekara.
A cewar tsohon gwamnan jihar Anambra, ’yan takarar shugabancin ƙasa huɗu na da cancanta da gogewar da ta dace wajen tafiyar da al’amuran ƙasa. Ya yi iƙirarin ba zai ba da shawara ko a kan wani daga cikinsu ba.
Ngige ya bayyana ‘yan takarar shugaban ƙasa da suka haɗa da Alhaji Abubakar Atiku na jam’iyyar PDO, da Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC, da Peter Obi na jam’iyyar LP, da kuma Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP a wata hira da manema labarai a ranar Laraba,garinsu Alor, ƙaramar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra.
Ministan ya kuma ba da gudummawa ga tsofaffi, zawarawa, da mabukata a unguwar.
KU KUMA KARANTA:A mai da hankali a Noma don rage Talauci da Yunwa – Obasanjo
Ngige ya sanar da ɗimbin jama’ar da suka hallara a harabar cocin St. Mary’s Pavilion da ke Alor cewa tun a watan Satumba gwamnatin tarayya ta bukaci ministocin su koma gida don taimakawa jama’arsu.
Ya ce bai kamata a ɗora matsalar abinci da makamashin da ƙasar ke fama da shiba kan gwamnati mai ci domin ta shafi ƙasashen duniya baki ɗaya, ba Najeriya kaɗai ba.
Ngige ya musanta kalaman Obasanjo na cewa Najeriya ta samu koma baya sosai tun bayan da ya hau mulki a shekarar 1999.
[…] KU KUMA KARANTA: Ba Buhari ya kawo talauci ba – Ngige ga Obasanjo […]