Baƙuwa ta sace jariri awa 3 da haihuwarsa a asibiti

0
204

Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa.

Ana zargin baƙuwar ta sace jaririn ne da haɗin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kaɗan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata.

Aminiya ta gano bayan haihuwarsa da misalin ƙarfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka miƙa jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su.

Wani ganau da ya nemi a ɓoye sunasa ya ce, bayan sun dawo ɗakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata baƙuwa, wadda ake zargin sun haɗa baki wajen sace jaririn.

A cewarsa, “’yar uwar mai jegon ce ta ce mata za ta koma gida ta ɗauko cajar wayarta da ta manta; shi ne ta haɗa ta da wata mata da za ta zauna da su kafin ta dawo ,” wadda ake zargin ita ce ta sace jaririn.

Sace jaririn daga ɗakin masu jegon da misalin karfe 6 na safe, awa uku da haihuwarsa ya jefa ɗaukacin jami’ai da sauran mutanen asibitin cikin al’ajabi.

Wata ’yar uwar mai jegon da ta nemi a ɓoye sunanta, ta tabbatar cewa, ’yar uwarsu ce kawo wa mai jegon wata baƙuwa, ta kuma damƙa mata jaririn.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga a Taraba sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa

A cewarta, ba su yi aune ba, sai dai aka nemi jaririn da baƙuwar — wadda ya yi zargin matsafiya ce — suka rasa, sun yi layar zana.

Ta ce, “Ba mu ga ɓarauniyar jaririn ba, wannan wane irin rashin imani ne, mace ta shiga asibiti ta yaudari duk ’yan ɗakin da masu tsaron ƙofa cewa za ta yi masa wanka, amma ta tsere da jariri. Duniya ta zama abin tsoro!”

Mai jegon, Malama Wasira Suleiman, wadda ke zubar da hawaye, ta ce “wadda aka kawo domin ta taimaka wajen kula da jaririn, ita ce ta sace jaririn da na ɗauka a cikina wata tara.”

Malama Wasira ta roƙi Gwamnatin Jihar Nasara da hukumar gudanarwar Asibitin DASH da hukumomin tsaro su taimaka su ceto jaririn nata ba tare da komai ya same shi ba.

Mahaifiyar jaririn ta bayyana cewa, “saboda ba ni da karfin da zan iya yi wa kaina komai” aka kawo matar a matsayin ’yar aiki — idan mai jegon tana buƙatar wani abu, ko sayen magunguan idan an buƙaci hakan.

A cewarta, bayan an bar matar ce ta buƙaci yi wa jaririn wanka, amma ta ce ta bari sai ’yar uwarta ta kawo kayansa.

Amma duk da haka matar ta nace cewa tana da kayan da za a lulluɓe shi idan aka yi wankan, a ƙarshe da mai jegon ta amince matar ta yi masa wanka, sai daga baya aka ce mata a sace jaririn nata.

“Wahalar da na sha na wata tara ba shi da misali, don haka babu abin da za a faɗa min da zan haƙura; ƙarfe biyun dare aka yi mini tiyata fa,” in ji mai jegon.

Muƙaddashin Shugaban Sashen Kula da Masu Juna Biyu na Asibitin DASH, Dalhatu Arafat ya bayyana taƙaicinsa kan lamarin yana mai cewa haka bai taɓa faruwa a asibitin ba.

A cewarsa, bayan an yi wa mai jegon aiki ta haihu da misalin karfe 3 na asubahin Talata aka kai ta ɗakin masu jego tare da mai kula da ita.

Ita kuma ta kawo wata baƙuwar da ba ta sani ba domin kula da su, za ta je gida ta ɗauko wani bu.

“Abin takaici, baƙuwar ta ɗauki jaririn da cewa za ta yi masa wanka, daga nan ta yi layar zana da shi, abin da mu a asibitin muka sani ke nan,” in ji shi.

Amma ya ce duk waɗanda ake da alaƙa da sace jaririn suna hannun ’yan sanda ana bincike domin gano baƙuwar da ta sace jaririn.

Dalhayu Arafa ya ce, “sai da muka ƙira kowa, saboda wannan ne karo farko a haka ya faru a nan” kuma waɗanda aka kama sun haɗa da ’yar uwar mai jegon da ta kawo baƙuwar da wasu ma’aikatan asibitin da ke aiki a lokacin da abin ya faru.

Duk wanda aka samu da hannu za mu sallame shi mu miƙa shi ga hukuma, domin zama darasi ga masu irin wannan hali.

“Za kuma mu ƙara amfani da kyamarorin CCTV domin ɗaukar duk wani motsi a cikin ɗakunan marasa lafiya,” in ji shi.
!

Leave a Reply