Atiku Ne Zai Iya Farfado Da Darajar Kasar Nan – Haruna Kofar Wambai

0
464

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

WANI dan gwagwarmaya kuma mai kaunar ci gaban Kasar nan Kwamared Haruna Kofar Wambai ya ce Najeriya zata sami ci gaba na gaskiya idan aka zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2023.

Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar su da wakilin mu a Kano, inda ya bayyana cewa ko shakka babu, Atiku Abubakar yasan matsalolin kasar n kuma zai yi kokari sosai domin ganin an magance su ta yadda al’amura zasu inganta.

Ya ce “idan Atiku Abubakar ya zamo shugaban kasa, za a sami ci gaba ta kowane fanni na zamantakewar al’umma duk da irin kalubalen da ake ciki na tattalin arziki da kuma tsaro, tare da fatan cewa yan Nijeriya zasu zabi Wazirin Adamawa Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023.”

Kwamared Haruna Kofar Wambai, ya kuma sanar da cewa ya kammala dukkanin shirye-shiryen da suka wajaba domin fara zagaye sashen arewacin kasarnan tare da bayyana irin alherin dake tattare da zaben Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa kafin tsallakawa Jihohin kudanci.

A karshe, Kofar Wambai, ya yi amfani da wannan rana wajen yin godiya ga Wazirin Adamawa Atiku Abubakar saboda kishin kasa da yake da shi a matsayinsa na kwararren dan siyasa kuma masanin makamar aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here