Andy Uba ya raba abinci ga Musulmai masu azumi

0
246

Jigon jam’iyyar APC a jihar Anambra, Andy Uba, ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar Azumin watan Ramadan na bana, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koyi da kyawawan ɗabi’u na rashin son kai, da sadaka da soyayyar juna kamar yadda addinin ya karantar.

Mista Uba, wanda ya yi magana a ranar Litinin ɗin da ta gabata a lokacin raba abinci ga mabuƙata don buɗa baki a watan Ramadan a Abuja, ya kuma yi ƙira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya yi iyakacin ƙoƙarinsa wajen ganin haɗa kan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da ƙabila, addini, ko karkata ga jam’iyar siyasa ba.

Ya ce kiran ya zama wajibi domin samar da ƙasa mai zaman lafiya da ci gaban ƙasa domin amfanin kowa. “Ina taya Musulman Najeriya murnar zagayowar watan Ramadan na wannan shekara.

KU KUMA KARANTA: Ramadan: Gwamnatin Kano ta amince da hutun mako 3 ga makarantu

Mu yi tunani tare da kwaikwayon kyawawan halaye na son juna, sadaka da sadaukarwa kamar yadda ake samu a cikin watan Ramadan.

“Ta hakan ne za a samu zaman lafiya da ƙaunar juna wanda hakan zai sa Najeriya ta samu zaman lafiya da samun ci gaba ta kowane fanni.

“Ina kuma ƙira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya gaggauta ɗaukar matakai da za su haɗa kan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da ƙabilarsu, addininsu ko aƙidar siyasa ba. Hakan zai shirya wa ‘yan Najeriya tudun mun tsira kamar yadda ya yi alƙawari,” in ji Mista Uba.

Leave a Reply