Ana zargin ɓarkewar cutar gubar Dalma a jihar Zamfara

0
4
Ana zargin ɓarkewar cutar gubar Dalma a jihar Zamfara

Ana zargin ɓarkewar cutar gubar Dalma a jihar Zamfara

Cutar da ta bayyana ta fi tasiri akan yara ƙanana. Daga cikin alamomin cutar, tana kumbura wa yara ciki Sosai. mai kula da al’amuran Lafiya a matakin farko a karamar hukumar Bunguɗu, Bashiru Muhammad Bungudu ya ce, lamarin yayi Kamari a kauyuka da dama, kuma ta na bayyana ne a jikin kananan yaran.

wakilin Muryar Amurka a Zamfara Abdulrazak Bello Kaura ya ruwaito cewa Bashir ya ce “Yara ‘Yan shekara biyar zuwa sha biyu suna kamuwa da cutar, cikin su yana kumbura kamar Kwarya, suna fama da zazzabi da kasala da kuma Amai.”

KU KUMA KARANTA:Cikin kwanaki uku, cutar kwalara ta kashe mutane 60 a Sudan ta kudu

Dr. Nafisa Muhammed Maradun Kwamishiniyar Lafiya ta jihar Zamfara, ta bada tabbacin bullar cutar, inda ta ce ya zuwa yanzu kimanin kananan yara 102 ne suka kamu da cutar kuma hudu daga cikin su sun riga mu gidan gaskiya.

A zantawar da Abdulrazak yayi da Dr.Nafisa Maradun, ta ce “Daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta dauka, akwai tura kwararru don gano nau’in cutar da kuma bude cibiyar kula da marasa lafiya inda za mai da hankali akan kula da cututtuka na musamman da kuma Matakan hana yaduwar cutar.”

Ta kara da cewa, lamarin yafi muni a kananan hukumomi, wadanda suka hada da Maradun, Bakura, Talata Mafara, Gummi, Bukkuyum, Maru, Bungudu da kuma Tsafe duka a cikin jihar Zamfara.

Leave a Reply