An yi ta ka-ce-na-ce tsakanin Isra’ila da Iran bayan mahukunta a Tehran sun yi alƙawashin yin ramuwar gayya sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ofishin jakadancinsu da ke birnin Damascus na Syria, yayin da hukumomi a Tel Aviv suka sha alwashin yin raddi.
Hayaniyar da ta kaure tsakanin Isra’ila da Iran ta yi ƙarami ranar Laraba, inda Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Katz ya wallafa wani gargaɗi ga Iran a shafukan sada zumunta.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, da harshen Hebrew da Persia wanda kai-tsaye ya tura wa Shugaban Addinin Iran Ali Khamenei, Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Katz ya yi barazanar yin martani idan Iran ta kai hari a Isra’ila.
“Idan Iran ta kai hari a cikin ƙasarmu, Isra’ila za ta mayar da martani ta hanyar kai wa Iran hari,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: Biden ya yi alƙawarin kare Isra’ila daga harin ramuwar gayya na Iran
Katz ya fitar da sanarwar ce jim kaɗan bayan Khamenei ya yi jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci sallar idi a Tehran, inda ya ce “gwamnatin shaiɗanu ta yi kuskure kuma dole a hukunta ta.”
Khamenei na bayani ne game da zargin da ake yi wa Isra’ila da hannu a harin da aka kai wa ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus ranar 1 ga watan Afrilu.