Daga Idris Umar, Zariya
A wani zama na musamman da aka gudanar a ɗakin taron tsohon gidan gwamnati, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya miƙa wannan saƙo a madadin gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa, wanda ya tafi ziyarar aiki ƙasar Amurka. Gwamnan ya umurci mataimakin gwamnan da gudanar da zama na musamman da dillalan man fetur na Jihar Katsina domin lalubo bakin zaren warware matsalar ƙarancin mai da ake fama da shi a jihar.
Malam Faruk Lawal ya jaddada matuƙar damuwar Gwamnati dangane da wannan al’amari tare da bayyana shirin gwamnatin jihar Katsina na haɗa kai da ƙungiyar IPMAN domin kawo ƙarshen wannan matsala. Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace don kawar da duk wani cikas ga samar da man fetur a jihar.
Da yake jawabi bisa ga ƙiran mataimakin gwamnan, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa IPMAN reshen jihar Katsina, Alhaji Abbas Hamza, ya bayyana wasu abubuwa da suka haifar da ƙarancin man fetur.
KU KUMA KARANTA: Matatar mai ta Ɗangote ta soma sayar da fetur a Najeriya
Ya yi nuni da cewa, cire tallafin man fetur ya sanya ‘yan kasuwa da dama cikin halin ƙaƙa-ni-kayi, lamarin da ya shafi yadda suke samar da kayan kamar da. Bugu da ƙari, ya shaida cewa yan ƙungiyar ta IPMAN na bin gwamnatin tarayya ‘kuɗaɗen dakon man fetur’ wanda shi ne babban abin da ya janyo ƙarancin man fetur ba a Katsina kaɗai ba har ma a faɗin ƙasar nan.
Bugu da ƙari, Alhaji Abbas ya bayyana cewa rashin samun isassen man fetur daga ma’ajiyar man fetur (depot) musamman a watannin farko na shekarar 2024 ya ƙara janyo matsala wajen ƙarancin man fetur a jihar. Ya kuma bayyana rufe wasu gidajen mai da ke kusa da kan iyaka da Najeriya da kuma hana sayar da man a galan a matsayin ƙarin ƙalubale.
Da yake mayar da martani, Malam Faruk Jobe ya yi ƙarin haske kan cewa dokar hana sayar da man a jarkoki ta shafi ƙananan hukumomin jihar takwas ne kawai saboda ƙalubalen tsaro. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Safana, Batsari, Ɗanmusa, Ƙanƙara, Faskari, Sabuwa, Ɗandume, da Jibia. Mataimakin Gwamnan ya yi ƙira ga ƙungiyar IPMAN da ta yi aiki don amfanin al’umma tare da rage tsadar farashin Man fetur a Jihar.
A ƙarshe ya tabbatar wa ‘yan kasuwar man fetur ɗin cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin warware taƙaddamar da ke tsakanin Gwamnatin Tarrayya da Ƙungiyar cikin lumana da gamsarwa.