An yi jana’izar babban ɗan Gwamnan Nasarawa da Allah Ya yiwa rasuwa

5
420

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya rasa ɗansa Hassan Sule wanda ya rasu a garin Lafia da yammacin ranar Alhamis, 26 ga watan Janairun 2023.

Marigayin wanda ya auri matarsa ​​ta farko, a watan Yunin shekarar da ta gabata, shi ne babban ɗan Gwamna Sule. Hassan mai shekaru 36.

Rasuwar ɗan gwamnan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Adra ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a. Sanarwar ta ce, “Mai Girma, Abdullahi A. Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa, a madadin iyalansa, ya sanar da rasuwar ɗansa, Hassan Sule, wanda abin bakin ciki ne ya faru a ranar Alhamis 26 ga watan Janairu, 2023.

KU KUMA KARANTA:Allah Ya yima Dr. Goni Abba Kaka rasuwa

Hasan ya rasu yana da shekaru 36 a duniya. An yi jana’izar marigayi Hassan a Gudi da ke ƙaramar hukumar Akwanga a yau Juma’a da karfe 10 na safe.

Yayin da yake mishi addu’a

A halin da ake ciki, Shugaban zartarwa na karamar hukumar Akwanga, Safiyanu Andaha, ya bayyana matukar kaɗuwarsa da rasuwar ɗan gwamnan tare da jajanta wa iyalansa kan rasuwar Hassan.

“A madadin iyalaina, karamar hukumar Akwanga da al’ummar Mada land, ina so in mika sakon ta’aziyyarmu ga Gwamna Abdullahi Sule, da iyalansa da kuma ɗaukacin majalisar sarakunan gargajiya ta Gudi bisa wannan babban rashin.”

5 COMMENTS

Leave a Reply